<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>125</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu Ubangijinmu yana gun Uba yanzu,
 Yana shirya mana wurin zama can.
 Wata rana, wata sa'a, za ya dawo duniya,
 Za ya fyauce Masu Binsa nandanan.

[V2]
 KORUS
 Muna jiran Sarkinmu, muna duban hanyarsa
 Ko da rana ya sauko, ko da dare ya iso,
 Sai ya iske mu da shirin karbarsa.

[V3]
 2) Kana daɗi za mu ji, za mu ga Ubangiji,
 Muna zamanmu tare har abada.
 Babu sauran ƃacin rai, farinciki ne kaɗai,
 Kullum murna za mu yi, ba fasawa.
 Korus

[V4]
 3) Ƴanuwa, ku zo yanzu, Yesu za ya wanke ku,
 Za ya kyauta muku rai har abada.
 Zo ku bi Mai Cetonku, faɗa masa laifinku,
 Shi ya shirya muku gafara tun dā.
 Korus</lyrics>
<title>Yesu Ubangijinmu Yana Gun Uba Yanzu LW125</title>
</song>